27 Yuli 2020 - 11:29
Musawi: Al’ummar Iran Ba Za Ta Taba Mancewa Da Kungiyar Munafikai Ta ( MKO) Ba Wacce Ta Sayar Da Kasa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Abbas Musawi wanda ya gabatar da taron manema labaru na mako-mako a yau Litinin ya yi ishara da farmakin “Misad” ko kuma madakata, wanda dakarun kare juyin musulunci su ka dakila yunkuri na karshe na kungiyar munafikan ta MKO a ranaku na karshe na kallafaffen yaki.

ABNA24: Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kara da cewa; A wancan lokacin da kungiyar ta munafikai ta ke kan ganiyar karfinta, kuma take samun taimakon kasashen waje, ba ta iya cimma wani abu ba a kasa, balle kuma da a wannan lokacin da tsufa ya kamata.

Abbas Musawi ya ci gaba da cewa; Al’ummar Iran sun ki jinin kungiyar ta MKO saboda sun zama abokan gaban al’umma, don haka ba za a taba mantawa da su ba a matsayin wadanda su ka sayar da kasarsu.

342/